Nasarar Abba Nasarar Al'ummar Kano ce--Abdul Bashir

 Nasarar Abba Nasarar Al'ummar Kano ce--Abdul Bashir


Daga Rabiu Sanusi



An bayyana Nasarar Gwamna Abba Kabir Yusuf nasara ce ta al'ummar jihar Kano baki daya a lokacin da kotun koli ta tabbatar ma gwamnan kujerar sa.


Batun ya fito ne daga bakin shugaban Kasuwannin Abubakar Rimi da aka fi sani Sabon Gari da da Galadima Alhaji Abdul Bashir a wata ziyara da manema labarai suka kai masa ranar litinin.


Shugaban Kasuwannin ya kara da cewa babu abinda yakamata ace yanzu a yi ma mai girma gwamna da ya wuce Addu'a da zai samu damar cigaba da aikin alkhairi da ya faro tun farko.


Abdu Hussain wanda ya cigaba da bayyana ayukan da gwamna Abba Kabir ya faro tun farkon hawan sa wannan kujera a matsayin wata nasara da ta samu jihar Kano ta al'umma ce baki daya.


"A zahirin gaskiya muna kara godiya ga mai girma shugaban darikar kwankwasiyya na duniya bisa hangen nesa wajen zaba ma Al'ummar Kano mutumin kirki mai iri dabi'ar sa watau Alhaji Abba Kabir.


MDn ya kuma tabbatar da wasu daga cikin ayukan sa da ya fara na sulhunta matsalolin da suka yi katu tu da ya gada a wannan tsohon shugaban kasuwar da ya gabata.


Kazalika ya dora da irin kokarin da gwamna ya ke wajen aikace-aikace daban-daban da aka sa gaba da zummar tabbatar da cigaban Al'umma da kuma dorewar zaman Lafiya a wannan jiha mai albarka.


Daga karshe ya bukaci jama'a da su taimaka wajen cigaba da addu'o'in da zasu kara taimakawa wajen samun cigaban da ake nema musamman yadda Allah yaba jihar Kano dan Amana.

Post a Comment

0 Comments